Skip to content
1 Tarihi 15:2-15

1 Tarihi 15:2-15

2
Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.”
3
Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.
4
Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa.
5
Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120;
6
daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220;
7
daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130;
8
daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200;
9
daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80;
10
daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112.
11
Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa.
12
Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da ’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa.
13
Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.”
14
Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila.
15
Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options