Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Glory of God: Moses

9 ayoyi · 22 fannoni

Ayoyi game da Moses

  1. Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.”

  2. Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai.

  3. Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.”

  4. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.

  5. A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce.

  6. Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.”

  7. Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa.

  8. Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci,

  9. nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”