Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nut
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon.
Na gangara zuwa cikin itatuwan almon don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya ko rumman suna fid da furanni.