Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Neophytes

6 ayoyi

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta.

  2. Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.

  3. “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba.

  4. ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai.

  5. Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba.

  6. Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi.