Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Juniper Tree
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.”
Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci. Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.”