Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Innocency: Contrasted with guilt

5 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Contrasted with guilt

  1. Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.

  2. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.

  3. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”

  4. Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”

  5. Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”