Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cherubim: In Ezekiel's vision of the temple
Ayoyi game da In Ezekiel's vision of the temple
an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. Zānen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu,
fuskar ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe, ɗaya fuskar kamar ta zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zāna su dukan a jikin bangon haikalin kewaye.
Daga ƙasa zuwa daurin ƙofa, an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a waje na wuri mai tsarki.