Tsallake zuwa abun ciki

Zephaniah

6 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Zephaniah

  1. Babban hafsan ya kwashi Serahiya babban firist, da Zefaniya na biye da shi a girma, da matsara ƙofofi uku.

  2. Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa,

  3. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya,

  4. Zefaniya firist kuwa, ya karanta wasiƙar annabi Irmiya.

  5. Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.”

  6. Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su.