Skip to content

Zabura 75

Godiya da Hukuncin Allah Mai Adalci 1–3

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce. Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.
2
Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.
3
Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela

Gargaɗi ga masu fahariya da girman kai 4–8

4
Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.
5
Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”
6
Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.
7
Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.
8
A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.

Nasarar masu adalci 9–10

9
Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,
10
wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.