Zabura142
Listen to this chapter
0:00
0:00
Kukan Ƙunci Daga Kogo
1
Maskil ne ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce. Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.
2
Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata.
Matsaloli da Tarkuna Sun Mamaye Ni
3
Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko.
4
Duba ta damata ka gani; babu wanda ya kula da ni. Ba ni da mafaka; babu wanda ya kula da raina.
Ubangiji Ne Mafakata Kadai
5
Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.”
6
Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai.
7
Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni.
Settings
Reading style
Typeface
Font size px
Reading width chars
Options
Study note