Skip to content

Zabura128

Albarkar Masu Tsoron Ubangiji

1
Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
2
Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.

Wadata a Gida da Iyali

3
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
4
Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.

Albarku Daga Sihiyona da Ga Isra’ila

5
Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
6
bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options