Zabura124
Listen to this chapter
0:00
0:00
1
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,
2
da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,
3
sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;
4
da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.
5
Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.
6
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.
7
Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.
8
Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Options
Study Note