Zabura1
Listen to this chapter
0:00
0:00
Hanyar masu adalci
1
Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
2
Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.
3
Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
Ƙaddarar marasa ibada
4
Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.
5
Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.
6
Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading style
Typeface
Font size px
Reading width chars
Options
Study Note