Ishaya4
Listen to this chapter
0:00
0:00
1
A wannan rana mata guda bakwai za su cafke namiji guda su ce, “Ma ciyar da kanmu mu kuma yi wa kanmu sutura; ka dai bari mu ce kai ne mijinmu. Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.”
2
A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila.
3
Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima.
4
Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta.
5
Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa.
6
Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Options
Study Note