Skip to content
Zakariya 7:4-10

Zakariya 7:4-10

4
Sai maganar Ubangiji Maɗaukaki ta zo mini ta ce,
5
“Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi?
6
Kuma sa’ad da kuke ci kuke sha, ba kanku kuke yi wa shagali ba?
7
Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ”
8
Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa,
9
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.
10
Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options