Waƙar Waƙoƙi 5:6-8
6
Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi. Zuciyata ta damu da tafiyarsa. Na neme shi amma ban same shi ba. Na yi ta kiransa amma bai amsa ba.
7
Masu gadi suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni. Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni; suka ƙwace gyalena waɗannan masu gadin katanga!
8
’Yan matan Urushalima, ina roƙonku, in kun sami ƙaunataccena me za ku ce masa? Ku ce masa na suma saboda ƙauna.
Settings