Waƙar Waƙoƙi 5:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ƙawaye Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.
2
Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”
3
Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?
4
Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar; zuciyata ta fara juyayi a kansa.
Settings