Skip to content
Waƙar Waƙoƙi 4:9-11

Waƙar Waƙoƙi 4:9-11

9
Kin saci zuciyata, ’yar’uwata, amaryata; kin saci zuciyata da hararar idanunki, da dutse mai daraja guda na abin wuyanki.
10
Ƙaunarki abar farin ciki ne, ’yar’uwata, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi gamsuwa, ƙanshin turarenki kuma ya fi duk wani kayan yaji!
11
Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata; madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki. Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options