Skip to content
Romawa 10:4-13

Romawa 10:4-13

4
Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.
5
Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”
6
Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi),
7
“ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu).
8
Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.
9
Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.
10
Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.
11
Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.”
12
Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi,
13
gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options