Romawa 10:18-21
18
Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji. “Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya, kalmominsu kuma har iyakar duniya.”
19
Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce, “Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba; zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.”
20
Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni; Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.”
21
Amma game da Isra’ila ya ce, “Dukan yini na miƙa hannuwana ga mutane marasa biyayya da masu taurinkai.”
Settings