Skip to content
Ru’uya ta Yohanna 9:1-7

Ru’uya ta Yohanna 9:1-7

1
Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis.
2
Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama.
3
Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya.
4
Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani.
5
Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum.
6
Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu.
7
Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options