Ru’uya ta Yohanna 1:17-19
17
Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe.
18
Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.
19
“Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba.
Settings