Zabura 84:1-10
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!
2
Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.
3
Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.
4
Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela
5
Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.
6
Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.
7
Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.
8
Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Sela
9
Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka.
10
Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye.
Settings