Skip to content
Zabura 75:4-8

Zabura 75:4-8

4
Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.
5
Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”
6
Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.
7
Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.
8
A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options