Skip to content
Zabura 7:1-5

Zabura 7:1-5

1
Wani shiggayiyon ta Dawuda, wanda Ya Rera wa Ubangiji game da Kush mutumin Benyamin. Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,
2
in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba.
3
Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana,
4
in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,
5
to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. Sela
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options