Skip to content
Zabura 69:1-5

Zabura 69:1-5

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata
2
Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.
3
Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.
4
Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba.
5
Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options