Zabura 68:7-18
7
Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, Sela
8
duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila.
9
Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji.
10
Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.
11
Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa,
12
“Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima.
13
Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.”
14
Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon.
15
Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.
16
Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada?
17
Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.
18
Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.
Settings