Skip to content
Zabura 64:1-2

Zabura 64:1-2

Addu’ar neman ceto daga maƙiyan ɓoye

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.
2
Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta.

Duba kuma

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Zabura 59:2

    Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.
    daga aya ta 2
  • Zabura 143:9

    Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka.
    daga aya ta 2
  • Irmiya 11:19

    Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
    daga aya ta 2
  • Zabura 31:20

    Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi.
    daga aya ta 2
  • Zabura 109:2

    gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.
    daga aya ta 2
  • Zabura 109:3

    Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili.
    daga aya ta 2
  • Zabura 27:5

    Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.
    daga aya ta 2
  • Irmiya 18:23

    Amma Ya Ubangiji, ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni. Kada ka gafarta musu laifofinsu ko ka shafe zunubansu daga gabanka. Bari a tumɓuke su a gabanka; ka yi da su sa’ad da kake fushi.
    daga aya ta 2
  • Zabura 3:1

    Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!
    daga aya ta 2
  • Zabura 56:6

    Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.
    daga aya ta 2
  • Makoki 3:55

    Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.
    daga aya ta 1
  • Makoki 3:56

    Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
    daga aya ta 1
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options