Zabura 55:16-19
16
Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.
17
Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.
18
Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.
19
Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.
Settings