- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Zabura 55:12-15
12
Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.
13
Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,
14
wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.
15
Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.
A cikin nassin nan
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Duba kuma
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
Zabura 41:9
Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.daga aya ta 122 Sama’ila 15:12
Yayinda Absalom yake miƙa hadaya, ya aika a kira Ahitofel mutumin Gilo, mai ba wa Dawuda shawara, yă zo daga Gilo garinsa. Ta haka makircin ya ƙara ƙarfi, masu bin Absalom kuma suka yi ta ƙaruwa.daga aya ta 13Mika 7:5
Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.daga aya ta 13Irmiya 9:4
“Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne.daga aya ta 13Zabura 42:4
Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki.daga aya ta 14Zabura 59:13
ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Seladaga aya ta 15Yohanna 13:18
“Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’daga aya ta 12Ayyukan Manzanni 1:18
(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo.daga aya ta 15Ayyukan Manzanni 1:20
Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’daga aya ta 15Zabura 9:17
Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah.daga aya ta 15Zabura 64:7
Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi.daga aya ta 15Zabura 109:6
Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.daga aya ta 15
Bayanin Nazari
Settings