Zabura 49:10-14
10
Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
11
Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
12
Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
13
Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Sela
14
Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.
Settings