Skip to content
Zabura 34:1-7

Zabura 34:1-7

1
Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
2
Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.
3
Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.
4
Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.
5
Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
6
Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.
7
Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options