Zabura 31:1-5
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.
2
Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona.
3
Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.
4
Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata.
5
Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.
Settings