Zabura 22:22-31
22
Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka.
23
Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!
24
Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako.
25
Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.
26
Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!
27
Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa,
28
gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai.
29
Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba.
30
Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima; za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji.
31
Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi.
Settings