- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Roƙon ƙarshe da bege na har abada
Zabura 17:13-15
Roƙon ƙarshe da bege na har abada
13
Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.
14
Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.
15
Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.
A cikin nassin nan
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Duba kuma
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
2 Korintiyawa 3:18
Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.daga aya ta 15Mattiyu 5:6
Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.daga aya ta 15Zabura 11:7
Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.daga aya ta 15Zabura 4:6
Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?” Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.daga aya ta 15Zabura 4:7
Ka cika zuciyata da farin ciki sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.daga aya ta 15Zabura 16:11
Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.daga aya ta 151 Yohanna 3:2
Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.daga aya ta 151 Yohanna 3:3
Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.daga aya ta 15Ishaya 26:19
Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.daga aya ta 15Filibbiyawa 3:21
shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.daga aya ta 15Zabura 65:4
Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki.daga aya ta 15Ayuba 22:18
Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.daga aya ta 14
Bayanin Nazari
Settings