Zabura 147:12-20
12
Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.
13
Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.
14
Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
15
Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri.
16
Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.
17
Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?
18
Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.
19
Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.
20
Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.
Settings