Zabura 145:21
Ana nuna aya 21 tare da mahallin da ke kewaye.
18
Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
19
Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.
20
Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su.
21
Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.
Settings