Zabura 145:1-7
1
Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.
2
Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
3
Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
4
Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.
5
Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
6
Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.
7
Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki.
Settings