Skip to content
Zabura 119:1-8

Zabura 119:1-8

1
Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
2
Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
3
Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.
4
Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.
5
Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!
6
Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.
7
Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.
8
Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options