Karin Magana 7:21-27
21
Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
22
Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
23
sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
24
Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
25
Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
26
Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
27
Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.
Settings