Karin Magana 4:1-9
1
Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi.
2
Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.
3
Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,
4
ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.
5
Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
6
Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
7
Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
8
Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
9
Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
Settings