Skip to content
Ƙidaya 7:30-35

Ƙidaya 7:30-35

30
A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa.
31
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
32
ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
33
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
34
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
35
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options