Ƙidaya 7:12-17
12
Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.
13
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri ne, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
14
ya kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
15
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
16
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
17
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.
Settings