Ƙidaya 7:1-9
1
Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
2
Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.
3
Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.
4
Ubangiji ya ce wa Musa,
5
“Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”
6
Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.
7
Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu,
8
ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.
9
Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
Settings