Ƙidaya 26:5-11
5
Zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila, daga Hanok; kabilar Hanokawa; daga Fallu; kabilar Falluyawa;
6
daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Karmi, kabilar Karmiyawa.
7
Waɗannan su ne kabilan Ruben; jimillarsu ta kai 43,730.
8
Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab,
9
’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji.
10
Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa.
11
Amma fa, zuriyar Kora ba tă mutu ba.
Settings