Ƙidaya 26:28-37
28
Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.
29
Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.
30
Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;
31
daga Asriyel, kabilar Asriyelawa; daga Shekem, kabilar Shekem;
32
daga Shemida, kabilar Shemadawa; daga Hefer, kabilar Heferawa.
33
(Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)
34
Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700.
35
Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu, daga Shutela, kabilar Shutelawa; daga Beker, kabilar Bekerawa; daga Tahan, kabilar Tahanawa.
36
Waɗannan su ne kabilan Shutelawa, daga Eran, kabilar Eranawa.
37
Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500. Waɗannan su ne kabilan Yusuf ta wurin kabilansu.
Settings