Skip to content
Ƙidaya 21:10-20

Ƙidaya 21:10-20

10
Isra’ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a Obot.
11
Sai suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim a hamadar da take fuskantar Mowab, wajen fitowar rana.
12
Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered.
13
Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa.
14
Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na tuddan Arnon,
15
da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”
16
Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.”
17
Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa, “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya! Rera waƙa game da ita,
18
game da rijiyar da ’ya’yan sarki suka haƙa, rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.” Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana,
19
daga Mattana, suka tafi Nahaliyel, daga Nahaliyel, suka tafi Bamot,
20
daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options