Ƙidaya 2:17-18
17
Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da Tentin Sujada za su kasance a tsakiyar sansani sa’ad da aka tashi tafiya. Za su kama hanya kamar yadda aka dokace su su zauna a sansani, kowa a wurinsa a ƙarƙashin ƙa’idarsu.
18
Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud.
Settings