Ƙidaya 17:1-7
1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.
3
A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.
4
Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.
5
Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”
6
Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.
7
Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.
Settings