Skip to content
Ƙidaya 16:16-22

Ƙidaya 16:16-22

16
Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can.
17
Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.”
18
Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada.
19
Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron.
20
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
21
“Ku ware kanku daga taron nan don in gama da su nan take.”
22
Amma Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka tā da murya suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin dukan ’yan adam, za ka husata da dukan taron ne, bayan mutum ɗaya ne ya yi zunubi?”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options